ORIGINAL RESEARCH ARTICLE | July 27, 2022
The Contrastive Analysis of “Laugh” Verbs in English and Chinese
Shang Jing, Li Yuan
Page no 204-208 |
10.36348/sijll.2022.v05i07.001
“Laugh” verbs rank almost first when people express their emotions. There are many “laugh” verbs in English, for learners with a relatively low proficiency level, it is quite difficult to choose the appropriate one to describe their states of mind. Due to their subtle differences, it is more difficult for learners to grasp their usage and meanings. This present paper aims to analyze the differences of some widely used “laugh” verbs through componential analysis.
ORIGINAL RESEARCH ARTICLE | July 30, 2022
Mawaƙa A Idon Hausawa: Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim
Abu-Ubaida Sani, Aliyu Hamma, Ibrahim Aliyu, Kachalla Aliyu Abubakar
Page no 209-216 |
10.36348/sijll.2022.v05i07.002
Hausawa na ɗaya daga cikin al’ummu da Allah ya azurta da ɗimbin mawaƙa. Tun inda aka fito, Bahaushe na amfani da waƙa a kusan dukkan ɓangarori ko al’amuran rayuwarsa. Wannan ya haɗa da sana’o’i (noma da saƙa da dukanci da farauta da sarkanci da ƙira da makamantansu), da kuma zamantakewa da bukukuwa da gyaran muhalli da ma sauran sha’anonin da rayuwar Bahaushe ke ƙunshe da su. Sai dai kamar yadda akan ce; “Idan kiɗa ya canza, rawa ma sai ta canza,” haka ma siga da salon waƙoƙin Hausa na canzawa tare da canjin zamani. A yau zamani ya kai, an samu mawaƙa da dama da ke amfani da kayan kiɗa na zamani yayin rera waƙoƙinsu. Sai dai wani abu shi ne, mawaƙan ƙasar Hausa na fuskantar tsangwama. Sau da dama matsayinsu ga idon jama’a ba ya wuce maroƙa ko limamen shashanci. Wannan ne ya sanya mawaƙa da dama ke rera waƙoƙi da ke nuna ƙorafinsu ga hakan. Wannan takarda ta nazarci ɗaya da cikin waɗannan waƙoƙi mai suna Waƙar Ranar Mawaƙa wanda Fati da Kasim suka rera. Sakamakon nazarin na nuna cewa; mawaƙa na fuskantar tsangwama a ƙasar Hausa. Sannan al’umma ba ta tallafa wa waɗannan mawaƙa ta fuskar shawarwari da sauran abubuwa da suka dace. Daga ƙarshe an ba da shawarwari da suka haɗa da, a riƙa jawo mawaƙa jiki tare da ƙarfafa musu guiwa da nusar da su kan samar da waƙoƙi masu amfani ga al’umma ta fuskar ilimi da zamantakewa.