Scholars International Journal of Linguistics and Literature (SIJLL)
Volume-5 | Issue-08 | 217-228
Original Research Article
Dangantakar Jigogin Wasu Labaran Magana Jari Ce Da Na Tatsuniyoyin Hausa
Abdulbasir Ahmad Atuwo, Abdurrahman Faruk
Published : Aug. 4, 2022
Abstract
Idan dai mutum ma’abocin karatun rubutattun labaran Hausa ne, ko mai sha’awar sauraro ko karatun tatsuniyoyin Hausa ne, babu shakka zai riƙa ganin wasu kamannu tsakanin wasu rubutatttun labaran Hausa da kuma tsatsuniyoyi na Hausa. Wannan dalili ne ya sa wannan takarda ta yi tsokaci a kan kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin rubutattun labaran Hausa da tatsuniyoyin Hausa. Taken wannan takarda shi ne, “Dangantakar Jigogin Wasu Labaran Magana Jari Ce da Na Tatsuniyoyin Hausa.” Manufar takardar ita ce, kwatanta dangantakar da ke akwai tsakanin wasu labaran da ke cikin Magana Jari Ce I - III da tatsuniyoyin Hausa ta fuskar jigogi, wato saƙonnin da suke ɗauke da su. An karanta wasu ayyukan masana da suka yi a kan fagagen tatsuniyoyi da rubutattun labaran Hausa. An kuma karanta littafin Magana Jari Ce I-III a matsayin dabaru da hanyoyin gudanar da bincike. An ɗora wannan bincike a kan Ra’in Tsarin Adabi (Structural Theory) na Propp (1928). Bayan an ƙare binciken, sai aka gano cewa, akwai kyakkyawar alaƙa ta fuskar jigogi tsakanin wasu labaran Magana Jari Ce I-III da tatsuniyoyin Hausa. Wannan alaƙa kamar yadda aka gano ta samu ne saboda rubutattun labaran Hausa sun tusgo gyauronsu ne daga tatsuniyoyin Hausa. Haka kuma, mawallafin littafin Magana Jari Ce I-III wato Abubakar Imam ya daɗe yana sauraron tsatsunoyin Hausa daga bakin kakanninsa tun yana yaro ƙarami kamar yadda kowane yaro ke tashi da sauraron su a ƙasar Hausa. Wannan babu shakka ya tasiranci tunanin Abubakar Imam wajen gina littafin Magana Jari Ce I-III.