SUBMIT YOUR RESEARCH
Scholars International Journal of Linguistics and Literature (SIJLL)
Volume-4 | Issue-09 | 282-287
Review Article
Waiwayen Ginshiƙan Bukatun Rayuwar Maguzawa
Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Published : Sept. 11, 2021
DOI : 10.36348/sijll.2021.v04i09.003
Abstract
Wannan bincike ya yi nazari ne a kan yadda al’ummar Hausawa suke gudanar da muhimman al’adun matakan rayuwarsu. A ƙoƙarin fayyace waɗannan ginshiƙai na rayuwa kamar yadda suke a kowace al’umma, nazarin ya kalli irin tanadin da Maguzawa suke yi musu a al’adance. Waɗannan abubuwa kuwa su ne abinci da muhalli da sutura da hanyoyin tattalin arziki da makamai da kuma hanyoyin samar da magunguna. Manufar wannan bincike ita ce a tabbatar da cewa, su ma Maguzawa al’adarsu ita ta tanadar musu yadda suka shimfiɗa rayuwarsu dangane da wasu ginshiƙai na rayuwa. Haka kuma nazarin yana da manufar fayyace yadda Maguzawa suke amfani da fasaharsu wajen samar wa kansu abin da ya zama dole su tanada kamar sauran al’ummu na duniya. Babbar hanyar da aka bi wajen gudanar da wannan nazari ita ce hira da dattijan Maguzawa ta fuskar shekaru domin tsamo abin da za su iya tunawa kuma waɗanda al’adunsu suka tabbatar dangane da waɗannan ginshiƙai na rayuwa. Haka kuma an yi nazarin littattafai da kundayen da aka rubuta musamman waɗanda suka shafi al’adun Maguzawa. Daga ƙarshe, nazarin ya gano cewa, Maguzawa sun yi amfani da abubuwan da suka samu a wuraren da suke zaune wajen shimfiɗa wa kansu al’adu cikin sauƙi da kuma samar wa kansu duk abin da suke bukata waɗanda suka zama dole rayuwa ta amfana da su. Wannan tanadi da suka yi, ya yi tasiri a rayuwarsu kuma ya taimaka musu wajen dogaro da kai.
Scholars Middle East Publishers
Browse Journals
Payments
Publication Ethics
SUBMIT ARTICLE
Browse Journals
Payments
Publication Ethics
SUBMIT ARTICLE
This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.
© Copyright Scholars Middle East Publisher. All Rights Reserved.