SUBMIT YOUR RESEARCH
Scholars International Journal of Linguistics and Literature (SIJLL)
Volume-4 | Issue-08 | 249-253
Review Article
Sááyèn Tsoron Cutarwa A Al’adun Hausawa
Dr. Nura Lawal, Dr. Yakubu Aliyu Gobir
Published : Aug. 23, 2021
DOI : 10.36348/sijll.2021.v04i08.005
Abstract
A wannan takarda an yi magana ne dangane sááyè a mahangar bori. Daga cikin abubuwan da aka yi tsokaci a kansu akwai; sááyè da bori, sannan kuma aka yi magana dangane da sááyèn tsoro a mahangar ‘yanbori da kuma sááyèn tsoro na wasu cututtuka a mahangar Hausawa. Haka kuma, a wannan takarda an yi amfani da ra’in Brown da Levinson (1987) mai suna Ra’in Ladabin Zance [1]. Wannan ra’i, da kuma ayyukan da suka biyo bayansa, sun tabbatar da sááyè muhimmin ɓangare a cikin al’adun al’umma, wato ta fannin cuɗanya domin nuna ladabi da ɗa’a da kunya da nisanta da kuma dangantaka. Har ila yau, waɗannan abubuwa (ladabi da ɗa’a da kunya) sanannu ne a al’adu da kuma tunanin kowace al’umma. Hakan ta sa sááyè yake taka muhimmiyar rawa wajen cuɗanya tare da ƙoƙarin inganta da kare mutuncin mutane. Wannan ra’i ya dace da yadda al’ada take tafiya tare da hikimomin amfani da matanonin sááyè wajen cuɗanya da kuma aiwatar da wasu al’adunsu. Har wa yau, an yi la’akari da wasu muhimman matakai na wannan ra’i da suka haɗa da: ma’ana da asali da rukunin al’ada da kuma yanayi ko lakacin yin al’adar. Haka kuma, a wannan takarda, an lura cewa, yin sááyè a wannan siga yakan ƙara cusa aƙida da kuma yin imani da wasu abubuwa. A wannan takarda an gano, cewa wannan al’ada ta sááyèn tsoro, wasu Hausawa suna amfani da ita a matsayin rigafi. Hakazalika, sááyèn tsoro, musamman a wajen ‘yanbori, yakan taimaka masu wajen samar da magunguna da kuma kyakkyawar alaƙa da aljanu a yanayin aiwatar da ayyukansu na bori.
Scholars Middle East Publishers
Browse Journals
Payments
Publication Ethics
SUBMIT ARTICLE
Browse Journals
Payments
Publication Ethics
SUBMIT ARTICLE
This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.
© Copyright Scholars Middle East Publisher. All Rights Reserved.