SUBMIT YOUR RESEARCH
Scholars International Journal of Linguistics and Literature (SIJLL)
Volume-8 | Issue-10 | 234-246
Review Article
Yarfe a Tarihin Siyasar Jam’iyyu a Ƙasar Hausa: Duba Cikin Rubutaccen Zube
Jibril YUSUF, Abu-Ubaida SANI
Published : Nov. 5, 2025
DOI : https://doi.org/10.36348/sijll.2025.v08i10.001
Abstract
Manufar wannan takarda ita ce nazartan yadda ‘yan siyasa suke amfani da abubuwa na ɓatanci ga abokan hamayyarsu na siyasa. Tunanin wannan takarda ya taso ne duba da yadda ‘yan siyasa suka mayar da wannan abu tamkar in babu shi to siyasar ma ba za ta yiwu ba. Wannan ya sa aka ga dacewar a shiga cikin ayyukan adabi na rubutaccen zube a gani shin ‘yarfe’ yana da asali ne tun kafuwar siyasar jam’iyyu ko kuwa bai daɗe da samuwa ba? An yi nazarin yarfe a cikin tarihin siyasa da aka kundace a cikin ayyukan rubutaccen zube. An ɗora binciken kan ra’in ‘Tarihanci’ inda ya yi jagorancin zaƙulo tarihin yarfe a harkokin siyasar ƙasar Hausa. Takardar ta gano cewa, yarfe abu ne da ya ginu a cikin siyasar jam’iyyu tun daga farkon lamari. Bugu da ƙari, har yanzu ana amfani da shi domin neman ƙarin mabiya da kuma shafa wa abokan hamayyar siyasa kashin kaji, wanda hakan kan taimaka ga samun nasara ko faɗuwa a zaɓe.
Scholars Middle East Publishers
Browse Journals
Payments
Publication Ethics
SUBMIT ARTICLE
Browse Journals
Payments
Publication Ethics
SUBMIT ARTICLE
This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.
© Copyright Scholars Middle East Publisher. All Rights Reserved.